Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shi dai dan Muammar Gaddafi ya daukaka kara a gaban wannan kotu kan matakin da hukumar zaben kasar ta dauka na kin amincewa da takararsa saboda tanade-tanaden doka.
Hukuncin kotun ya faramtawa magoya bayan Seif Al Islam rai a kotun da ke Sebha, dake da tazarar kilomita 650 kudu da birnin Tripoli.
An dai zargi dan tsohon shugaban kasar da cin zarafin bil adama a lokacin guguwar neman sauyin data yi awan gaba da mulkin mahaifinsa a shekarar 2011, kuma tun lokacin kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nemansa ruwa a jallo.
342/